Accessibility links

​Shugaban Amurka Barack Obama yayi gargadin cewa Amurka zata mayar da martani mai karfi idan har Koriya ta Arewa tayi gwajin makamin Nukiliya na hudu, lamarin da wasu manazarta suke gani kamar zai iya yiwuwa a kwanaki masu zuwa.

A lokacin da yake magana da kafofin yada labaran Koriya ta Kudu kafin ya isa babban birin kasar Seoul, Mr. Obama yace “Koriya ta Arewa fa bazata karu da komai ba, idan tayi gwajin Nukiliya na hudu, sai ma kara ware ta da sauran kasashen duniya zasu yi.”

Itama gwamnatin Koriya ta Kudu tayi gargadin cewa fa kamar Koriya ta Arewa na shirin gwada makamin Nukiliya na a babban ma’asanantar Nukiliyar kasar, kuma wasu kungiyoyin binciken Amurka sun goyi bayan wannan kazafi.

Manazartar dangantakar Amurka da Korea a jami’ar Johns Hopkins ta harkokin kasa da kasa tace hotunan da tauraron dan Adam ya dauko na masana’antar Nukiliyar Koriya ta Arewa mai suna Punggye, sun nuna kamar akwai wani abu da ake shirin yi, kuma ta iya yuwa gwajin Nukiliyar ne.

Ta kara da cewa hotunan da aka dauka Larabannan, sun nuna kamar motocin da ake amfani da su wajen kyasta ashanar Nukiliyar a harabar da ake gwada makamashin na kasar, kuma an ga irin wadannan motoci kafin gwajin da Arewan tayi a watan Febrairun 2013.

Sai dai manazartar tayi kashedin cewa babu tabbacin ko za’a gudanar da wannan gwajin saboda ba ko yaushe bane ake fahimtar me shuwgabannin kasar suke shirin yi.
XS
SM
MD
LG