Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo Yana Shiga Tsakani Don Kawo Karshen Rikicin Tigray


 Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da tsohon Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta sun je kasar Afirka ta Kudu a matsayin masu shiga tsakani a tattaunawar sulhun da kungiyar Tarayyar Afirka ta kulla tsakanin gwamnatin tarayyar Habasha da wakilan yankin Tigray.

Gwamnatin tarayyar Habasha da shugabannin yankin Tigray sun fara taron ne a Nairobi babban birnin kasar Kenya jiya Litinin don tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Tarayyar Afirka suka rattabawa hannu a makon jiya a Afirka ta Kudu.

Bangarorin na tattaunawa kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da kuma samun tallafin abinci da magunguna da ake bukata a yankunan da aka kwashe shekaru biyu ana yaki.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

Gwamnatin Habasha da dakarun Tigray sun kafa layin wayar tarho na mussaman don taimakawa wajen tabbatar da tsagaita bude wuta a makon da ya gabata, kuma bangarorin biyu sun gana a Kenya jiya litinin domin wani sabon zagayen tattaunawa kan aiwatar da yarjejeniyar.

Babban mai shiga tsakani na kungiyar ta AU, Olusegun Obasanjo, ya shaida wa taron manema labarai a Nairobi cewa, "alama ta farko a gare ni na ci gaban da aka samu bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, ita ce, yadda aka yi musayar layin waya ta musamman a tsakaninsu.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

A cewar wani jami'in da ke da masaniya kan tattaunawar, layin wayar zai magance duk wani rikici da ya barke tare da daidaita batun raba gardama.
Yarjejeniyar dai ta bukaci kawo karshen rikicin na tsawon shekaru biyu da kuma kai agajin jinkai ga al'ummar yankin na Tigray.

Jagoran masu shiga tsakani na gwamnatin Habasha Redwan Hussein ya ce abu ne mai muhimmanci a sake hade al'ummar Tigray da sauran sassan kasar.

“A wuraren da ba mu da damar yin amfani da su, dole ne mu hanzarta sake haɗa da kuma gyara ayyukan sadarwa, makamashi da tsarin banki. Amma kafin nan, mutanenmu suna bukatar abinci da magunguna, kuma muna kokarin hanzarta hakan,” inji shi.

Yakin dai ya raba miliyoyi da muhallansu tare da kashe wasu dubbai.

XS
SM
MD
LG