Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Habasha Ta Kai Hari Da Ya Kashe Mutane Uku 'Yan Gudun Hijirar Eritrea


Ethiopia
Ethiopia

Wani hari ta sama da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira a yankin Tigray na arewacin kasar Habasha ya kashe 'yan gudun hijirar Eritriya uku.

Ciki wadanda suka mutu har da yara biyu, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a Yammacin jiya Alhamis, a jerin hare-hare na baya-bayan nan da suka kunshi asaran rayukkan fararen hula.

Harin na ranar Laraba an kai shi ne akan sansanin 'yan gudun hijira na Mai Aini da ke kusa da garin Mai Tsebri na kudancin yankin Tigray, inji MDD.

"An kashe 'yan gudun hijirar Eritrea uku, biyu daga cikinsu yara kanana," in ji kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) Filippo Grandi a cikin wata sanarwa, inda ya kara da cewa wasu 'yan gudun hijira hudu sun jikkata.

Mai magana da yawun gwamnati Legesse Tulu da mai magana da kakakin rundunar sojan, Getnet Adane ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba. A baya dai gwamnati ta musanta zargin tana kai hari a kan fararen hula.

A ranar 30 ga watan Disamba, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce an kashefararen hula da dama a kudancin Tigray a hare-haren sama da aka kai a wancan makon, hare-haren da ta bayyana a matsayin "mafi muni da asarar rayuka da aka taba kaiwa tun watan Oktoba".

Yakin da aka kwashe watanni 14 ana gwabzawa a Arewacin kasar Habasha tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar fafatikar Tigrai (TPLF) da ta taba mamaye harakokin siyasar Habasha, ya yi sanadin mutuwar dubban fararen hula tare da raba miliyoyi da muhallansu.

A watan da ya gabata, sojojin Tigray sun janye daga yankunan da ke makwabtaka da su, wadanda suka mamaye a watan Yuli. Ana ci gaba da kai hare-hare ta sama a yankin na Tigray kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wani agajin jin kai da zai iya shiga yankin.

-Reuters

XS
SM
MD
LG