Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Mukaddashin Shugaban Kasa Na Kokarin Amso Sauran Mutanen Da Boko Haram Ta Sace


Ofishin mukaddashin shugaban najeriya ya ce yana nan yana ci gaba da matsa kaimi wajen tabbatar da an sako ‘yan matan chibok dama karin wadanda boko haram ke garkuwa dasu.

Baya ga daliban 'yan matan Cibok, da suka rage a hannun 'yan kungiyar boko haram a yanzu, kungiyar ta sace wasu mata da maza da kananan yara a sassa daban daban dake arewa maso gabashin Najeriya,

Ofishin mukaddashin Najeriya, ya bayyana cewa suna nan suna ci gaba da bada kokari domin tabbatar da kubutar da sauran 'yan makarantar da suka rage da kuma sauran wadanda lamarin ya rutsa da su, kamar yadda hadimin ofishin Alhaji Hafizu Ibrahim, ya bayyanawa wakilin muryar Amurka Hassan Maina Kaina.

Ya ce " ba lallai jama'a su san duk abubuwan da gwamnati ke yi ba, amma da ikon Allah jama'a zasu gani da idanunsu".

Yayin da ake kokarin ceto 'yan matan cibok, kwatsam sai kungiyar ta fito da waniu sabon bidiyo na yin garkuwa da wasu mata da suka kama a motar 'yan sandan Najeriya dake kan hanyar su daga Maiduguri zuwa Damboa.

Daga Abuja ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG