Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Mayar Da Martani Bayan Amurka Ta Soke Tallafin Da Take Bata


Ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mehmood.
Ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mehmood.

Pakistan tayi watsi da rahotanni da suke nuni da cewa Amurka ta soke tallafin soja na kudi dala milyan 300 da take baiwa kasar,tana mai cewa kudaden bashi ne da kasar take bin Amurka, wadanda ta ce ta kashe wajen yaki da ta'addanci.

Ministan harkokin wajen kasar Shah Mehmood, ne ya bayyana haka bayan da ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa ta soke baiwa Islamabad tallafin, saboda kasar ta gaza daukar matakai kan kungiyoyin 'yan ta'adda da suke cikin kasar.

Wannan sabon rikici da yake tashi a dangantakar da take kara tsami tsakanin kasashen biyu, yana zuwa ne ana saura kwanaki sakataren hakokin wajen Amurka Mike Pompeo da kuma baban hafsan hafsoshin Amurka Janar Joseph Dunford, su kai ziyara kasar dake kudancin Asiya.


A halin da ake ciki kuma, shugaban hukumar MDD dake tallafawa 'yan gudun hijira na falasdiu, yace hukumar zata ci gaba da tallafawa Falasdinawa, a kuma dai dai lokacin da Amurka ta bada sanarwar kawo karshen gudumawar kudi da take baiwa hukumar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG