Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP ta kira gwamnatin APC dake mulkin Najeriya ta sake salon tafiya


PDP

Babbar jami'yyar adawa a Najeriya PDP na ganin babu wani abun a zo a gani da gwamnatin APC tayi tunda ta kama mulkin kasar cikin shekara daya da ta wuce idan aka kwatanta da kalamun shugaba Buhari yainda yake fafutikar neman zabe

Barrister Ali Gulak wanda a da shi ne yake ba tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara akan harkokin siyasa ya kwatanta gwamnatin APC da tafiyar hawainiya.

Ali Gulak yace akwai bukatar shugaba Buhari ya sauya salon tafiyar gwamnatinsa tunda yanzu shugaba ne na kowa.

Yace da APC ce jam'iyyar adawa amma yanzu tana gwamnati yayinda PDP ce ta zama jam'iyyar adawa. Ali Gulak yace saidai har yanzu APC bata san itace a karagar mulki ba. Tana cigaba da farfaganda kamar tana adawa ko kuma tana neman zabe.

'Yan Najeriya suna cikin kunci. Babu abinci. Tattalin arziki ya rugurguje. Da kyar ake biyan albashin ma'aikata. A jihar Adamawa an yi wata hudu ba'a biya albashi ba.

Ali Gulak ya yadda an soma samun zaman lafiya amma kuma akwai wata babbar rashin lafiya wato yunwa wadda bata san babba da yaro ba. A kasuwa kowa barci yake yi domin babu mai saya balle a sayarwa.

Saidai 'yan APC a martanin da suka mayar suka ce ba abun mamaki ba ne idan 'yan PDP na kuka yanzu. Alhaji Ahmed Lawal sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC a jihar Adamawa yace ko yaron dake goye ya san an samu sauyi yanzu. A fannin tsaro an samu cigaba. Abun da shi ma shugaba Buhari ya tabbatar.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
APC
APC

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG