Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

QATAR 2022: Zakarun Gasar Cin Kofin Duniya Za Su Sami Kyautar Dala Miliyan 42


Yan wasan Argentina
Yan wasan Argentina

Zakarun gasar cin kofin duniya za su samu kyautar dala miliyan 42 daga asusun bayar da kyaututtukan FIFA na dala miliyan 440.

Kungiyar da ta yi rashin nasara a wasan karshe na ranar Lahadi tsakanin Faransa da Argentina za ta samu dala miliyan 30 daga asusun ta FIFA.

A lokacin da Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 2018, kasar ta samu dala miliyan 38 daga asusun kyaututtuka na FIFA dala miliyan 400.

Ba duka kudin ke zuwa wajen 'yan wasa ba, amma ana sa ran za su sami kudi mai yawa. ‘Yan wasan kasar Faransa irinsu Kylian Mbappé na shirin karbar biyan alawus na Euro 554,000 ($586,000) domin lashe wasan karshe, in ji jaridar L’Equipe ta kasar Faransa.

Kowace hukumar kwallon kafa ta kasa tana samun akalla dala miliyan 9 a matsayin kyauta don buga gasar cin kofin duniya ta bana, da kuma dala miliyan 1.5 ga kowannensu na kudin shirye-shiryen gasar.

Kungiyar Croatia da ta zo ta uku ta samu dala miliyan 27. Morocco wadda ta kare a matsayi na hudu za a ba ta dala miliyan 25.

Jimlar kudaden da FIFA ta samu a shekaru hudu da suka gabata ya kai dala biliyan 7.5, mafi yawan kudin da aka samu daga tallace-tallace na watsa shirye-shirye gami da tallace-tallacen tikiti da kuma baki.

XS
SM
MD
LG