Accessibility links

Ra'ayoyin Jama'a Akan Sanya Kayan Makaranta Dake Nuna Addinin Dalibi


hijab

Tun da gwamnatin jihar Osun ta fitar da wani tsarin barin 'yan mata Musulmai su sa hijab a makarantu har ma da wadanda asalinsu na mishan ne, anyi ta kai ruwa rana lamarin da ya haddasa zanga-zanga a jihar.

A jihar Osun gwamnati ta baiwa 'yan mata Musulmai damar sanya hijab zuwa makaranta kamar yadda addininsu ya tanada.

Dokar bata yiwa Kiristocin jihar dadi ba, musamman a makarantun da dama can sun samo asali ne daga mishan kamar yadda ta faru a makarantar Baptisti dake garin Iwo a jihar ta Osun. Lamarin dai ya tayarda yamutsi ba karami ba.

Wakilin Muryar Amurka Hassan Umar Tambuwal ya zagaya yaji ra'ayoyin jama'a kan wannan batun da ya raba al'ummar Osun gida uku wato Musumai da Kiristoci da masu bin addinan gargajiya.

Hassan ya fara da shugabannin Musulunci da na Kirista.Fasto Philip Miyango na Mijami'ar Baptist dake Sabo Ibadan da aka tambayeshi ko me ya gani game da maganar.

"Me ya sa suka yarda Musulmi da Kirista suka hadu a cikin makaranta. Da yake sun tabbatar su 'yanuwan juna ne Musulmi da Kirista suna nan a cikin makaranta daya ai batun hijab da Kirista ya sa nashi ba zai kawo damuwa ba. Ni idan mun lura zamu gani da cewa makarantar ya hadu da Kirista da Musulmi. Mu manta da maganar makarantar na mishan a'a. Tun da an hadu ya zama na mutum daya ne. Idan ya zama haka Kirista ko Musulmi ba zasu kawo wani doka wanda zai shafi addini ba. Duk doka da ya shafi addini zai kawo banbanci", a cewar Fasto Philip Miyango.

Shi ma Malam Abubakar Atiku Sabo Ibadan an yi masa tambaya dangane da sanya hijab a makarantar Baptist dake Iwo da bayanin cewa makarantar ta Kirista ce. Sai yace "Nawa tunane a nan shine duk da cewa makarantar na Kiristoci ne amma abun da na sani daga baya ta dawo karkashin gwamnati. Don haka da wanda ke Musulmi da wanda ba Musulmi ba yana da 'yanci a wannan ainihin makaranta din kuma yanzu zamani ne wanda an tabbatar cewa a tsarin mulkin Najeriya kowa yana da 'yancin da zai bayyana ainihin addinisa. Don haka, kamar yadda addini ya ce idan Musulmai zasu fita su rufe jikinsu ya zama wajibi su ma a basu dama su rufe jikinsu dai-dai da addinisu a wannan makaranta"

Malam Abubakar Atiku ya kara da cewa babu komi Musulmai su sanya hijabi su je wannan makarantar domin yana ganin 'ya'yan kirista suna sanya kros, wato alamar addini Kirista suna zuwa makarantu kuma makarantun bana Kiristoci bane na gwamnati ne. Yace Kirista da Musulmai suna da 'yanci a makarantar.

Amma wani yace tun da abun ya janwo tashin hankali kowa ya bar sa rigar addini domin a zauna lafiya. Haka ma Zainab tace a bar Musulmai su sa hijab dinsu kowa kuma a bari yayi addininsa.

XS
SM
MD
LG