Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Budewa Fararen Hula Wuta A Myanmar


Masu Zanga Zanga A kan Abinda Ya Faru
Masu Zanga Zanga A kan Abinda Ya Faru

A Myanmar, 'Yansandan kasar sun harbe tare da kashe akalla mutane 7 a jahar Rakhine mai fama da rigingimu.

Jami’ai suka ce akalla mutane dubu hudu ne suka zagaye wani ginin gwamnati a daren jiya talata a garin Marauk U, jim kadan bayan an kammala wani bikin tunawa da kawo karshen wata masarautar gargajiya da ake yi duk shekara, wacce ta shude fiye da shekaru dari biyu da suka wuce.

Tim Maung Swe, wanda shine gwamnan yankin, yace ‘Yansanda sun yi kokarin su tarwatsa mutanen, ta wajen harba albarusai na roba a iska, amma da mutanen suka ki bin umarnin, kuma suka fara kaiwa jami’an tsaro hari, jami’an tsaron sun bude wuta da albarusai na kwarai.

Kungiyar kare hakkin Bil’Adama ta Human Rights Watch ta yi kira da a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa da zai duba yadda lamarin ya kai ga amfani da albarusai na kwarai.

Kungiyar ta yi kira kan a horas da jami’an ‘Yansandan kasar wajen sanin hanyoyin shawo kan al’umma ba tare da amfani da makamai ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG