Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Yaki Da Shan Taba Sigari a Duniya


Wani Dan kasar Indiya na zukar taba sigari.
Wani Dan kasar Indiya na zukar taba sigari.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa sama da mutane Miliyan bakwai ne ke mutuwa a duk shekara sanadin matsalolin da suka danganci shan taba sigari, kuma tana kawo koma baya ga tattalin arzikin kasashe

Yau ranar 31 ga watan Mayu, rana ce da aka kebe domin yaki da shan tabar sigari a duniya, a saboda haka hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga gwamnatoci da su ‘dauki kwakkwaran matakan shawo kan matsalar shan taba sigari, domin kare lafiyar mutane da kuma tattalin arzikin kasashen.

Hukumar WHO wadda ta baiyana taba sigari a matsayin barazana ga ci gaba. Baya ga kashe sama da mutane Miliyan bakwai a duk shekara, wani kiyasi da aka yi ya nuna cewa kowacce shekara “taba cin kudi Dala Triliyan 1.4.”

Duk da matakan shawo kan matsalar taba sigari, rahotan da WHO ta fitar na yawan mutanen da suke mutuwa daga cututtukan da suka shafi taba sigari, yawancinsu mutanen da suka dade ne suna shan tabar, kuma zai ‘dauki lokaci kafin matakan da za a dauka su fara aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG