Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Na Neman Ba'asin Mutuwar Mikhail Lesin a Washington


Marigayi Mikhail Lesin, tsohon mataimakin masamman ga Shugaban Vladmir Putin
Marigayi Mikhail Lesin, tsohon mataimakin masamman ga Shugaban Vladmir Putin

Jami’an kasar Rasha sun koka da cewa hankalinsu na tashe ne a kokarinsu na samun bayanai game da mummunar mutuwar Mikhail Lesin, wani tsohon mataimaki ga shugaban kasar Vladmir Putin.

Jami’an sun ce an sami gawarsa ne a wani dakin Otal a nan Birnin Washington. Manyan shugabanni a Rasha sun yi magana jim kadan bayan fitar da sanarwar mutuwar Mista Lesin.

Inda Rashar ke neman gwamnatin Washington da ta yi mata bayanin yadda lamarin ya faru, domin an bayyana cewa mamacin ya mutu ne sakamakon masifar wahalarwa a watan da ya gabata.

Kakakin Ma’aikatar Wajen Rasha Maria Zakharova tace wannan bukatar bayani na tafe a cikin diflomasiyya don neman bayani.

Jami’an ‘yan Sandan Amurka a Washington sun bayyana cewa a lokacin da aka sami gawarsa, an gano cewa ya sha wahalar raunuka a kansa, kafadu da kafafuwansa.

XS
SM
MD
LG