Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Na Shirin Maida Martani Ga Takunkuman Amurka


Shugaban Rasha, Vladmir Putin

Kasar Rasha tace ba zata zuba ido ta kyale takunkuman da Amurka da Canada da kuma Kungiyara Tarrayar Turai suka kakaba mata a kan harin da ita Rashan ta kaiwa jiragen ruwan Ukraine guda uku a shekarar 2018, a cikin ayyukanta na mamayar yankin Crimea a gabashin Ukraine.

Ma’aikatar bitalmalin Amurka ta fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a dake cewa, takunkuminta na auna wasu ‘yan kasuwa guda shida ‘yan kasar Rasha da kamfanoni takwas a matsayin martani ga ci gaba da ayyukan tashin hankali da Rasha ke yi a Ukraine.

Sakataren kudi a Amurka Steve Mnuchin ya fada a cikin sanarwar cewa, wannan aikin hadin gwiwa da Amurka tayi da kawayenta Canada da Kungiyar Tarrayar Turai suna sake jaddada wannan takunkumai mai muhimmanci ne a matsayin martani ga Kremlin na bijirewa sharudodjin kasa da kasa da kuma rashin mutunta Ukraine a matsayin kasa mai cin gashin kanta da kuma rashin kiyaye darajar yankunanta.

Sanarwar ta kara da cewa, Amurka da kawayenta na duniya ba zasu nade hannu su zubawa Rasha ido ta ci karenta ba babbaka a kasar Ukraine ba tare da an ja mata burki ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG