Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha ta yi tur da hare hare kan Syria


Shugaban Rasha Rasha Vladiir Putin

Rasha ta yi Allah wadai da jerin hare-haren da aka kai a Syria, wadanda ta yi ikrarin za su maido da hanun agogo baya a kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya a kasar.

A wata sanarwa da ya fitar, Ministan harkokin wajen kasar Rasha, ya ce wadannan hare-hare da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa, na bukatar kasashen wajen su maida martani

Wasu hare-hare da aka kai a birnin Damascus a jiya Lahadi sun halaka akalla mutane 83, yayin da wani harin bam na daban ya kashe mutane 59 a Homs.

Yanzu haka Rashan da Amurka, na kokarin su rarrashi bangarorin da ke takaddama a kasar ta Syria, da su amince da wani sabon shirin tsagaita wuta.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry a jiya Lahadi, ya ce an cimma wata matsaya ta wucin gadi da kasar Rasha wacce za ta fara aiki nan da wasu ‘yan kwanaki

Kerry ya gana ne da twakaran aikinsa Sergie Lavrov ta wayar talho, inda ya ce bangarorin biyu sun amince da tsarin tsagaita wutar, ba tare da sun bayyana yadda za a tafiyar da shirin ba.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG