Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Samar Da Tsaro a Najeriya


A daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar wasu sassan Najeriya shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa za a murkushe 'yan ta'adda da masu aikata miyagun laifuka a kasar.

A lokacin da yake ziyarar kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai ta gudanar, shugaban ya tabbatarwa da al'umomin jihar aniyarsa ta murkushe 'yan ta'adda da masu aikta laifukan dake addabar kasar.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Juma'a, shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa mazauna garin Kaduna, karkashin rundunar sojojin Najeriya niyarsa na murkushe ayyukan ta'addanci a sassan kasar.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban ya yaba da irin tallafin da jihar Kaduna ke baiwa jami’an tsaro, inda ya bayyana cewa an kafa ma’aikatar tsaro ta cikin gida don gudanar da wannan aiki.

A nasa jawabin gwamna El-Rufai yayi kira da a kara daukar matakin soji domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.

Ya ce “Mun kashe makudan kudade don tallafawa hukumomin tsaro na tarayya a jihar domin inganta tsaro da rayuwar al’ummarmu.

"Amma akwai bukatar kara daukar matakan soji domin dakile ‘yan ta’addan da ke barazana ga mutanen mu, ''in ji shi.

Gwamnan Kaduna ya godewa shugaban kasar bisa ziyarar aiki da ya kai jihar Kaduna da kuma irin goyon bayan da yake bai wa jihar don ganin ci gaba.

XS
SM
MD
LG