Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Sun Gudanar Da Gangamin Kira a Fita Zabe a Fadin Amurka


Gangamin mata a Washington, DC.
Gangamin mata a Washington, DC.

Mata sun gudanar da gagarumin gangami jiya asabar a birane daban daban na fadin kasar da nufin karfafawa Amurka guiwa su fita zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar uku ga watan Nuwamba.

Mata sun sake tattaki yin gangami a Washington da wasu birane a nan Amurka a jiya asabar tare da niyar zaburar da Amurkawa su fito su fidda shugaba Donald Trump daga Mulki da kuma kin amincewa da wadda ya zaba mai ra’ayin rikau Alkali a Kotun Koli, Amy Coney Barrett bayan rasuwar mai ra’ayin sassauci Ruth Bader Ginsburg.

Kungiyar mata masu ra’ayin rikau su ma sun gudanar da gangamin a harabar kotun Kolin. Kungiyar da ke kiran kansu, mata masu ra’ayin kashin kansu,sun shirya gangamin ne da take “I’m with Her” wanda ke nufin ”Ina tare da Ita” don nuna suna tare da Barrett.

ana-hasashen-wanda-trump-zai-zaba-ya-maye-gurbin-ginsberg-a-kotun-koli

trump-ya-zabi-amy-coney-ta-zama-alkalin-babbar-kotun-koli

an-fara-zaman-tabbatar-da-amy-coney-barret-a-matsayin-alkalin-kotun-kolin-amurka

“Ba cewa ake yi kawai Trump ya sauka shike nan ba inji Darektar tattakin na Mata Rachel O’Leary a farkon fara gangamin na Washington. “Batu ne na cewa zamu cika alkawarin kasa ga dukkanmu. Kuma ya rage ga kowannenmu mu daukarwa kanmu wannan nauyin mu tabbatar da manufar kasarmu. Mu bada damar!”

Gangamin mata a Washington, DC
Gangamin mata a Washington, DC

Bisa ga takardar izinin hukumar kula da wuraren shakatawa ta kasa, masu shirya taron sun sa ran wadanda za su halarci gangamin za su kai tsakanin dubu 6 zuwa dubu 10 da zasu taru a Freedom Plaza a Washington a gangamin da aka gudanar da tsakiyar rana, inda suka yi tattaki zuwa harabar Kotun Koli suka karasa da aikawa da sakonnin kada ta kwana. Masu shirya gangamin sun ce burinsu na aika sakonnin shi ne kira ga jama’a su fito su kada kuri’a a zaben na 3 ga watan Nuwamba.

Masu shirya tattakin na Mata sun ce sun karfafa mahalarta su yi amfani da takunkumi da bada tazara domin kaucewa yada annoba. Sun kuma shawarci wadanda su ke zaune a bangaren da coronavirus tafi kamari kada su halarci gangamin. Sun kuma yi kira ga jama’a a duk fadin kasar da su shiga gangamin da ake yi a inda su ke maimakon tafiya nesa.

An gudanar da daruruwan irin wannan gangamin a fadin kasar a jiya Asabar da suka hada da wadanda suka gudana ta yanar gizo da motocin tafi da gidanka da nufin dakile yaduwar coronavirus. An kuma gudanar da irin wannan a Jami’ar Cornell, Kolejin da Ginsburg ta yi.

Gangamin mata a Washington, DC
Gangamin mata a Washington, DC

An gudanar da gangamin ne a daidai lokacin da jam’iyar Republican a Majalisar Dattijai take shirin fara kada kuri’a mako mai zuwa na tabbtar da Barret, wadda idan aka tabbatar da ita, za ta ba masu ra’ayin ‘yan mazan jiya rinjaye a Kotun koli inda zasu zama alkalai 6 , yayinda masu sassaucin ra’ayi suke da uku. ‘Yan jam’iyar Democrat suna fargaban cewa zaben Barret zai iya sa kotun ta sauke dokar da aka ba lakabi da "Roe V.Wade" wata doka da ta ba mata ‘yancin zubar da ciki.

An gudanar da irin wannan gangamin matan ne na farko a shekara ta 2017 lokacin da miliyoyin mata suka yin gangamin yin Allah wadai da rantsar da Trump shugaban kasa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG