Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Richarlison Ya Rattaba Hannu Kan Kwantiragin Shekara Biyar A Tottenham


Richarlison
Richarlison

Dan wasan ya kasance na hudu da kungiyar ta Tottenham ta yi cefanansu a wannan lokaci na bazara, baya ga Fraser Forster, Ivan Perisic da Yves Bissouma da ta siyo.

Dan wasan Brazil Richarlison ya rattaba hannun kan kwantiragin shekara biyar da Tottenham.

Kafafen yada labaran Birtaniya sun ruwaito cewa Tottenham ta sayi Richarlison ne akan kudi dala miliyan 73 daga Everton kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Dan shekara 25, Richarlison ya bugawa Everton wasanni 152 a dukkan gasar Ingila inda ya zura kwallaye 53.

Ya zura kwallaye 48 a gasar Premier a wasanni 173 da ya buga a gasar ga Everton da kuma Wtaford, kungiyar da koma bayan da ya baro Fluminense a 2017.

Dan wasan ya kasance na hudu da kungiyar ta Tottenham ta yi cefanansu a wannan lokaci na bazara, baya ga Fraser Forster, Ivan Perisic da Yves Bissouma da ta siyo.

Richarlison zai zamanto kari ga ‘yan wasan gaban kungiyar ta Tottenham wacce Antonio Conte yake horarwa, wanda a mafi yawan lokuta yake dogaro da Harry Kane da Son Heung-min wajen neman kwallaye.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG