Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Riek Marchar Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Kan Mukamin Taban Deng Dai


Mai Magana da yawun Madugun ‘yan Tawayen Sudan ta Kudu Riek Marchar, ya yi kira ga kasashen duniya da kar su yarda da shugabancin Taban Deng Dai, a matsayin wanda aka nada a mataimakin shugaban Salvar Kirr.

Mai Magana da yawun na Marchar, James Gadet, Dak yace yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakanin shugaban da mataimakin sa, ya ruguje ne bayan da shi Kirr ya yanke shawarar nada Taban Deng Gai, a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Deng, dai shine babban mai shiga tsakanin jamiyyar Sudan People’s liberation movement da gwamnati a birnin Juba wanda hakan ya kawo karshen rikicin dake tsakanin sassan biyu.

James Gadek, yace wannan yarjejeniyar ta ruguje ne sakamakon yakin da kasar ta sake tsundumawa, yayin da ake ci gaba da fada a wasu yankunan babban birnin kasar na Juba.

Domin ko sojojin gwamnatin sun kaiwa rundunar Marchar hari a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata kuma shugaba Salvar kirr ya karya yarjejeniyar dakatar da bude wa juna wuta, wannan yasa ba wani sauran yarjejeniyar dakatar da bude wuta inji Dak.

Dak, ya ci gaba da cewa muna kira da a samu wata rundunar da zata shiga tsakani domin ganin an kawo karshen wannan al’amari. Yace amma kuma idan ba haka ba zai zame muna wajibi mu shiga cikin birnin na Juba domin karbe ikon kasar.

Fada dai ya barke tsakanin ‘yan kasar ta Sudan ta kudu tsakanin magoya bayan Salvar Kirr da mataimakin sa Riek Marcher tun acikin shekarar 2013, wanda yayi dalilin mutuwar dubban mutane kana wasu sama da miliyan 2 suka rasa muhallain su.

XS
SM
MD
LG