Accessibility links

Rikicin iyaka ya barke tsakanin jihohin Gombe da Yobe inda an samu asarar rai daya wasu kuma da dama sun jikata

An samu barkewar rikici kan iyaka tsakanin jihohin Gombe da Yobe inda mutum daya ya mutu wasu da dama kuma suka samu rauni.

Rikicin ya samo asali ne kan mallakar wata gona dake gap da kan iyakan jihohin. Yayin da daya daga cikin wadanda suke takardama a kan gonar ya je cikinta sai mutane daga daya gefen kuma suka farmasa.

Wani mazaunin kauyen da abun ya faru ya fadawa wakilin Muryar Amurka cewa dama can maganar tana gaban sharia don haka ba dai-dai bane wasu daga wani gefen su shiga gonar da niyar mallakarta lamarin da ya kai ga gabza fada har mutum daya ya mutu wasu goma sha daya kuma sun samu rauni.

Yanzu dai 'yan sanda sun kama wasu kuma an jibge jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Abdulwahab Muhammed nada rahoto.

XS
SM
MD
LG