Accessibility links

Rikicin Shugabanci a Jam'iyyar APC ya Kunno Kai a Jihar Gombe

Yayin da take kokarin wawure 'yan jam'iyyar PDP rikicin shugabanci ya soma kunno,kai a jihohi daban daban a jam'iyyar APC. Na kwana kwanan nan shi ne na jihar Gombe.

Rikicin shugabanci ya kunno kai a jam'iyyar adawa ta APC a jihar Gombe yayin da wasu 'yan jam'iyyar ke korafin an hanasu shiga dakin taron jam'iyyar. Taron wanda mataimakiyar shugaban mata na kasa ta jam'iyyar Hajiya Amina Mohammed ta jagoranta shi ne irinsa na farko da aka gudanar a jihar Gombe.

Malam Abdullahi Kabo na cikin 'yan jam'iyyar da bai samu shiga dakin taron ba. Ya ce taro ne na jam'iyyarsu shi ya sa ya zo ya halarceshi amma aka hana shi shiga. Ya ce an ki gaya masu gaskiyar irin halin da jam'iyyar take ciki. Ya ce jama'a kamar wasu 'yan PDP suna tambaya yaya jam'iyyar domin suna son su shigo amma bai san abun da zai gaya masu ba. Ya ce abun mamaki shugabanninsu na APP da na ACN da na CPC sun zo amma sun wuje basu shiga taron ba. Ya ce to shi taron menene yake nufi.

Malam Musa Sale Aliyu Pindiga ya ce taron kamar almara ake yi . Idan ba almara ake yi ba yaya za'a ce an yi jam'iyyar hadaka wasu kalilan su zo suna yin abun da suka ga dama. Idan haka za'a yi tafiyar babu inda zasu je. Idan hadin kai ake so to yakamata a zo a yi magana da kowa a san inda aka sa gaba. Ba za'a yi da wasu ba a ce wasu kuma ba za'a yi dasu ba. Hakan ba zai kawo cigaba ba. Tun da aka kafa jam'iyyar APC wannan taron shi ne farko na shugabanninta domin ana yi ne a boye.

Da take mayar da martani Hajiya Amina Mohammed ta ce taron ba na kowa da kowa ba ne gaba daya duk da wai shi ne irinsa na farko a jihar. Ta ce taron na wadanda zasu shirya yiwa mutane ragista ne. Ta ce an bata sunayen wadanda ya kamata ta tattauna dasu kuma su ne ta tuntuba. Ta ce ba hanasu shiga a ka yi ba. Tun can ainihi an aiko da sunan wadanda za'a gana da su.

Abdulwahab Mohammed nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG