Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Kasashen Yankin Tafkin Chadi Ta Hallaka Mayakan Boko Haram 59


Sojojin dake fafatawa da 'yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi sun baza kayan yakin da suka kwace

Rundunar sojojin kasashen yankin tafkin Chadi dake fafatawa da mayakan Boko Haram na samun nasara matuka kuma kawana kwanan nan sojojin suka hallaka 'yan ta'adda 59, suka cafke wasu biyar tare da yin raga-raga da makanasu, da kanasu da rumbun abincinsu

Babban kwamandan sojojin kasashen yankin tafkin Chadi dake fafatawa da kungiyar Boko Haram Manjo Janar Lucky Irabor na Najeriya ya tabbatar da nasar da suke samu a farmakin da su keyi yanzu.

A cewarsa sun hallaka mayakan Boko Haram 59. Sun cafke wasu biyar a raye tare da karin wasu 'yan kunar bakin wake. Sun kuma cafke motocin 'yan ta'addan guda shida dake shake da makamai yayinda suka yi rugu-rugu da rumbunan abincinsu da kayan anfaninsu na yau da kullum.

A cewar Janar din aikinsu na samun nasara sosai kuma zasu ci gaba da murkushesu har sai sun ga bayansu, injishi.

Farmakin da aka sawa lakanin Operation Amni Fakat ya biyo bayan nasar da suka samu ne a wani Operation Ruwan Kada da suka yi a baya.

A cewar wani masanin tsaro Air Commodore Ahmed Tjjani Baba Gamawa nasarar bata zo masa da mamaki ba saboda sabbin dabarun yaki da yadda sojojin suka san wurin da kuma yadda karfin Boko Haram ya ragu ainun. Yawancin manyansu da kwararrunsu an kashesu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG