Accessibility links

Wata Rundunar Soja ta Musamman a Adamawa ta Kashe 'Yan Bindiga 13 ta Kwato Miliyoyin Naira da Suka Sata a Mubi

  • Aliyu Imam

Wata rundunsr dojojin Najeriya.

Kwamandan Rundunar ne ya bayyana haka a bikin maida kudin ga hanun 'yan kasuwan da aka yiwa fashi.

A Najeriya, wata rundunar sojin kasar ta musamman a jihar Adamawa, ta sami nasarar kashe ‘yan bindiga 13, ta kuma kwato samada da Naira milyan uku da tace ‘yan Boko Harama din suka yi fashinsu daga hanun ‘yan canji a kasuwar Mubi dake kan iyaka ranar 20 ga watan jiya.

Kwamandan rundunar leftanar kanal B. Martin ne ya bayyana haka a bikin mika kudin ga ‘yancin da aka yiwa fashin agarin Mubi.

Daga nan ya godewa jama’a saboda irin hadin kai da suke baiwa rundunar a kokarinta na yaki da masu tada fitina a yankin.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG