Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Halaka 'Yan Boko Haram 40


Air Commoder Ibikunle Daramola
Air Commoder Ibikunle Daramola

Hedkwatar Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun rugurguza wasu sansanoni biyu masu muhimmancin gaske na kungiyar mayakan Boko Haram.

Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola ya shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa biyo bayan amfani da kuramen jirage masu leken asiri, jiragen yakinsu, samfurin Alpha Jets sun rugurguza cibiyar tsara dabarun yaki na Boko haram, da kuma cibiyar ba da umarni na kungiyar da ke Izza a dajin Sambisa.

Air commodore Daramola, ya ce, kimanin mayakan na Boko Haram 40, da aka hango a sansanin farko kafin kai farmakin, duk baki daya an halaka su bayan harin.

Rundunar sojojin saman Najeriyar, ta ce za ta ci gaba da aiki tare da sauran dakarun kasar don kawo karshen 'yan ta'adda, da Boko Haram a Arewa maso gabas,

kuma kamar yadda tsohon babban hafsan hafsoshin rundunar dakarun kasar Air Marshal Al'Amin Dagash ke cewa, yana da kwarin gwiwar lalle sannu a hankali, mayakan Najeriya za su kawo karshen wadannan 'yan ta'addan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG