Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Gwamnan Bauchi Ya Yi Alkawarin Yin AIki Da Kwararru A Bauchi


Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi)

Zaben shekarar 2019 yazo da abubuwan ban al’ajabi da kuma mamaki da suka hada har da kwace mulki daga hannayen jam’iyu dake mulki suka koma hannun jam’iyun adawa kamar yadda suka faru a jihohin Bauchi dakuma Gombe da wasu wurare a Najeriya.

A jihar Bauchi jam’iyar PDP ta adawa itace ta kwace mulki daga hannun jam’iyar APC a bayan da ta shekara hudu tana mulki wanda wannan shine karon farko a tarihin siyasa jihar Bauchi inda gwamna mai ci yakasa samun damar yin tazarce.

Zababben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Kauran Bauchi tare da mataimakinsa, Sanata Baba Tela sun mika dubun godiya ga wadanda suka taimaka musu suka samu nasara a zaben da ya gabata. Saidai gwamnan da mataimakin sa sun tunasar da jama’ar su cewa akwai babban kalubale a gaban su. Ya ce dole ne su yi aiki tukuru kada su ba mutanen da suka basu wannan damar wanda ginshikin sa ne kawowa mutane Bauchi canji.

Sanata Bala ya yi alkawari cewa shi jami’an sa zasu aiki su kawo kudiri da zai fitar da mutanen jihar Bauchi daga mawuyacin hali da suke a ciki. Gwamnan ya ambato wasu matsaloli mutanen jihar ke fama da su, kamar talauci da wahala da tabarbarewar ilimi da harkar noma da sauran su, wanda ya ce zasu yi aiki domin fitar da al;ummar jihar a cikin su.

Ya ce gwamnatin sa zata yi amfani da kwararru da zasu taimaka mata wurin cimma burin kawo jihar Bauchi sama da sauran jihohi kamar yanda matsayin yake a baya. Kuma ya yi alkawarin ba zai aiki da gaba ba. Yace ko shakka babu wannan aiki ne mai wahala, a don haka sai bullo da tsare tsare masu inganci da kwarewa domin cimma wadannan muradu. Ya kuma yi kira ga jama’a a taya su da addu’a.

Wakilin mu Abdulwahab Mohammed ya hada jawabin sabon Gwamnan jihar Bauchi:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG