Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai An Ci Bashi Kafin a Iya Aiwatar Da Kasafin Kudin 2021 - Sanata Abdullahi


Sanata Yahaya Abdullahi Abubakar
Sanata Yahaya Abdullahi Abubakar

Bisa ga dukan alamu dole Najeriya ta nemi agajin da zai ba ta sararin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2021 na Naira tiriliyan 13.08 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa hadaddiyar majalisar kasa.

'Yan Najeriya dai sun fara bayyana ra'ayoyinsu game da kasafin kudin shekarar 2021 ne bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin wanda ya nuna cewa sai an ci bashin Naira tiriliyan 4.28 kafin a iya aiwatar da shi.

Sai dai wasu mahukuntan kasar sun bayyanaa cewa za a iya barin baya ba zani wajen neman nasarar cimma burin Shugaban kasa akan kasafin.

Sanata Abdullahi Abubakar Yahaya, mai wakiltar jihar Kebbi ta arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, ya nuna cewa lallai kafin a iya aiwatar da kasafin kudin sai an nemi bashi daga kasashen ketare.

Sanatan ya kara da cewa Najeriya ta dade ta na dogara kan shigo da kayayyaki daga kasashen ketare ba tare da ta yi tanadin gina masana'antunta ba, sai yanzu da aka samu wannan gwamnatin ne tunanin yin hakan ya taso saboda kasar ta samo hanyar yin dogaro da kanta kuma hakan ba zai yiwu ba a yanzu sai da bashi.

Shi kuma Sanata Ahmed Babba Kaita, mai wakiltar Katsina ta Arewa, ya ce ya na ganin ba lallai ba ne sai an samu wani jinkiri ko kuma koma baya wajen aiwatar da kasafin tunda ko yanzu an ware makudan kudade fiye da Naira biliyan 400 don tallafa wa al'umar kasa, kuma hakan na iya taimaka wa tattalin arzikin kasar domin za a samu ayyukan yi da yawa a fanin noma.

Babba Kaita ya kuma kara da cewa bangaren ilimi ya samu kaso mai tsoka a kasafin na badi da sama da Naira biliyan 100 idan aka kwatanta da kasafin bana da aka ba shi Naira biliyan 40 da doriya.

Amma kwararre a fannin tattalin arzikin kasa da kasa Shu'aibu Idris Mikati, ya ce ya na ganin kasar ba ta da karfin arzikin da za ta aiwatar da kasafin shi ya sa za ta ci bashi, kuma cin bashi ba aibu ba ne domin sai an yarda da kasa ake iya ba ta bashi.

Mikati ya kara da cewa bullar cutar coronavirus ta kawo karyewar tattalin arzikin kasashen duniya da dama, ciki har da Najeriya.

Abin jira a gani shi ne yadda kudin gangar danyen man fetur za ta kasance a kasuwar duniya daga yanzu zuwa badi, ganin cewa har yanzu ita ce hanya daya tilo ta samun kudaden shiga lalitar gwamnatin Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG