Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Da Hujja Zan Yarda Da Zargin Fyade Ga Fernando - Inji Fafaroma


Fafaroma Francis a Chile

Fafaroma Francis ya zargi wadanda wani Babban limamin coci yayi lalata da yara a Chile da yiwa Bishop din kage da suka ce ya kare wanda ake zargi.

Yayin da yake magana da manema labarai, kafin Fafaroma Francis ya bar kasar Chile zuwa ta Peru, yace har sai da wata kwakkwarar shaidar da zata nuna Bishop Juan Barros na da laifi wajen kare laifuffukan lalata da ake zargin Revarand Fernando Karadima kafin ya amince da batun.

Amma idan babu wata hujja, to zai ci gaba da kallon wadannan zarge-zarge a matsayin shaci fadi. Jawabin na Fafaroman ya dagula yunkurinsa na gyara kaurin sunan da Cocin Katolika tayi na aikata masha'a da yara, kuma ya girgiza wannan jawabin ya girgiza al’ummar kasar ta Chile.

Wanda ya jawo martini daga wadanda wannan matsalar ta shafa sun yi nuni da cewar wadanda ke zargin an yarda da zarginsu matuka a Fadar Paparoman da har ta kai jallin da aka yankewa Karadima hukuncin rai da rai na “Tuba hade da yin addu’a” akan laifuuffukan daya aikata a shekarar 2011.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG