Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatare Kerry Yayi wa Isra'ila da Falasdinu Kashedi


​Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace lokacin binciken gaskiya yayi, game da batun lalacewar tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da jami’an Palestine.

Da yake magana yau Juma’a daga garin Rabat, Kerry yace yana shirin bincika hanyoyin da za’a yi amfani da su wajen cigaba da neman zaman lafiya, dangane da abunda ya kira shawarwari na “da-na-sani” da duka bangarorin biyu suka yi.

Dama dai tattaunawar ta samu matsala ne tun bayan da Isra’ila ta cigaba da gine-gine a yammacin kogin Jordan, da kuma dakatar da sakin Fursunonin Palastinawa, da kuma cigaba da yunkuri da Palastine takeyi a MDD domin gani ta amince da ita.

Kerry ya dage akan cewa babu wani bangare daga cikin sassan biyu dake haramar fita daga cikin tattaunawar. Amma yace baza a cigaba da lalube a cikin duhu ba, inda ma yayi gargadin cewa akwai iyakar matakan da Amurka zata iya dauka, idan bangarorin biyu basu da niyyar yin abubuwan da suka dace domin samun zaman lafiya.
XS
SM
MD
LG