Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Na Nairobi Kasar Kenya


John Kerry, Sakataren Harkokin Wajen Amurka da Amina Muhammad, Ministar Harkokin Wajen Kenya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya na ziyara a birnin Nairobi na Kenya, inda ya ke ganawa da ministocin harkokin wajen kasashen gabashin Afrika, kan hanyoyin da za a bi domin kaucewa sake fadarwar Sudan Kudu cikin yakin basasa.

A yau Litinin Kerry ya gana da shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, gabanin ya hadu da ministocin harkokin wajen, domin ganin an dakile sake fanjamar Sudan Ta Kudu cikin wani sabon yakin basasa. Sudan ta Kudu dai ita ce ‘yar autar kasashen duniya.

Har ila yau Kerry da sauran ministocin harkokin wajen kasashen Afrika, za su tattauna kan rikicin Somalia, wacce ke shirin gudanar da zabukan ‘yan majalisu da na shugaban kasa.

Nan gaba a cikin wannan makon ne Kerry zai yada zango a Najeriya, kasar da mayakan Boko Haram suka kashe fiye da mutane dubu 20 tun daga shekarar 2009, sannan zai tsaya ma a Saudiyya, wacce ke jagorantar dakarun hadin gwiwa domin yakar ‘yan tawayen Houthi a kasar Yemen.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG