Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saliyo: Ana Zaben Shugaban Kasa a Zagaye Na Biyu


Wata mai kada kuri'a a zaben farko da aka yi ranar 7 ga watan Maris, 2018.
Wata mai kada kuri'a a zaben farko da aka yi ranar 7 ga watan Maris, 2018.

Ana zaben shugaban kasa a zagaye na biyu a kasar Saliyo bayan da 'yan takara 11 suka gaza samun adadin kuri'un da zai ba su nasara.

Masu jefa kuri’a a kasar Saliyo sun fita zuwa rumfunan zabe a yau Asabar, domin kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa a zagaye na biyu.

Ana sake zaben ne, bayan da dukkanin ‘yan takara 11 suka gaza samun kashi 55 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben farko, adadin da ake bukata kafin samun nasara.

A baya, an so a sake zaben ne a ranar Talatar da ta gabata, amma kuma aka jinkirta, saboda a bai wa wata kotun kasar damar sauraren karar da wani mamban jam’iyar All People’s Congress ya shigar.

Masu jefa kuri’ar, suna zabi ne tsakanin dantakarar jam’iyar mai mulki ta APC, Dr. Samura Mathew Wilson Kamara da kuma dan takarar jam’iyar Sierra Leone Peopl’es Party, Julius Maada Bio.

Kamara ya dasa manufofin yakin neman zabensa ne akan zai ci gaba da ayyukan da jam’iya mai mulki ta APC ke yi.

Sai dai ‘yan adawa na zargin jam’iyar mai mulki da badakalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye mulkinta, da kuma gazawa da ta nuna a lokacin barkewar cutar Ebola a shekarar 2014.

Wannan dai shi ne karo na biyu da dan takarar ‘yan adawa, Bio ya tsaya takara.

A shekarar 2012 ya fadi zabe bayan da shugaba mai ci Ernest Bai Koroma ya ka da shi.

Koroma zai sauka a mulkin ne saboda ya kammala wa’adinsa biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG