Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin NDA Ba Zai Karya Mana Kwarin Gwiwa Ba – Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Instagram/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Instagram/ Muhammadu Buhari)

“Wannan danyen aiki zai zaburar da dakarunmu wajen kawar da duk wasu muggan ayyuka, wanda sojojinmu suka kuduri aniyar aiwatarwa nan ba da jimawa ba.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kwalejin horar da dakarun kasar ta NDA da ke Kaduna, ba zai sanyaya gwiwar sojojin kasar ba, a maimakon haka ma, zai kara zaburar da su ne a yunkurin da suke yi na kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar.

Buhari ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Laraba.

“Wannan danyen aiki zai zaburar da dakarunmu wajen kawar da duk wasu muggan ayyuka, wanda sojojinmu suka kuduri aniyar aiwatarwa nan ba da jimawa ba.”

Babbar Hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya
Babbar Hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya

Buhari ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu yana mai addu’ar Allah ya ba su hakurin wannan rashi.

“Buhari ya sha alwashin cewa mutuwar dakarun ba za ta tafi a banza ba, domin za a dauki matakin da zai mayar da martanin da zai kawar da baragurbin da ke kasar.”

Shugaban na Najeriya ya kuma yi kira ga wadanda suke furta kalaman cusa kiyayya kan wannan al’amari, da su guji yin hakan yana mai cewa wannan lokaci ne da za a hada kai a yaki masu muggan manufofi.

Dakarun Najeriya a kwalejin NDA suna atisaye (Facebook/Dakarun Najeriya)
Dakarun Najeriya a kwalejin NDA suna atisaye (Facebook/Dakarun Najeriya)

A ranar Talata wasu ‘yan bindiga suka far wa kwalejin horar da sojojin Najeriya ta NDA inda suka kashe sojoji biyu suka kuma yi garkuwa da guda daya.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta sha alwashin daukan mummunan mataki akan ‘yan bindigar wadanda suka addabi jihar ta Kaduna wacce ta zama tamkar tungar ‘yan fashin daji a arewa maso yammacin kasar.

XS
SM
MD
LG