Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutum 700 Suka Mutu Sanadiyar Guguwar "Idai" - MDD


Wani mutum dauke da yaransa bayan da guguwar Idai ta ratsa ta yankin Beira a aksar Mozambique, Maris 23, 2019.

Masu ayyukan ba da agaji sun ce tabbas adadin mutanen da suka mutu a kasashen uku zai karu, yayin da ambaliyar ruwan ke janyewa.

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce jumullar adadin mutanen da suka mutu a wasu kasashen yankin kudancin Afirka sanadiyar mummunar guguwar da aka wa lakabi da "Idai" da ta abkawa yankin, ya haura mutum 700.

Sama da mutum 400 sun rasu ne a Mozambique, inda masu ba da agajin gaggawa ke ta kokarin taimakawa dubun dubatar mutane.

Ministan filaye da muhalli a Mozambique, Celso Correia, ya ce har yanzu “ana cikin wani mawuyacin hali, amma ana samun sauki.”

Ya kara da cewa akwai akalla mutum 1,500 da ke saman rufin gidaje da bishiyoyi, wadanda suke so a ceto su, sannan kusan mutum dubu 89 sun koma sansanin ‘yan gudun hijira.

Baya ga kasar ta Mozambique, akwai kasashen Zimbabwe da Malawi da su ma suke kokarin farfadowa daga wannan mummunar guguwa.

Masu ayyukan ba da agaji sun ce tabbas adadin mutanen da suka mutu a kasashen uku zai karu, yayin da ambaliyar ruwan ke janyewa.

Akalla mutum miliyan 1.7 wannan guguwa ta shafa, wacce ba a taba ganin guguwa mai karfinta a yankin ba cikin gwamman shekarun da suka gabata.

Facebook Forum

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG