Accessibility links

Samarda Wutar Lantarki Daga Rana


Samarda wutar lantarki ta anfani da karfin rana a wani kauye a Najeriya

Shugaban Najeriya ya amince a samarda wutar lantarki daga rana, ruwa da iska

Shugaban kasar Najeriya Ebele Jonathan ya bada karfin gwiwa da a kara yin nazari da gudanar da cikkaken bincike wurin anfani da makamashi na zamani domin a samarda wutar lantarki ba tare da dogara kan injina ba kamar yadda a ke yi yanzu.

Shugaban hukumar makamashi ta Najeriya Farfasa Eleji Derebala ya ce lallai gwamnati tana fatan kafin shekarar 2030 za'a rage dogara da anfani da injina da wajen kashi 30 cikin dari. Hakan zai yiwu ta yin anfani da rana da ruwa da iska wajen samun lantarki ba tare da samun wasu matsaloli ba. Wadannan abubuwa uku basa karewa. Yanzu dai gwamnati ta fara saka dimbin kudi domin a samu lantarki ta wadannan hanyoyin.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

XS
SM
MD
LG