Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Ta Fuskanci Fafata Gasar Cin Kofin Zakarun Turai


Xavi na Barcelona
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00

Xavi ya jagoranci atisayen Barcelona kafin Bayern Munich a gasar UCL a rukunin E.

Bari mu dubi abin da ke wakana a zagayen karshe na wasan league na zakaru a matakin rukuni, yayin da ya rage saura gurabe biyar daga cikin gurabe 16 da za a fafata akai, da kuma zakaru uku da har yanzu da ba a tantance ba a matakin rukuni rukuni.

GROUP E
Barcelona za ta fafata wasa da kungiyar Bayern Munich wadda dama tuni ta tsallake zuwa zagaye nagaba. Akwai yiwuwar cewa a karon farko cikin kakar wasanni ta 18, Barcelona ba za ta shiga zagayen wasan kwab-daya ba, wanda hakan zai zama wani babban naushi ga wannan kulub na Catalan mai tangal tangal, a kakar wasanta ta farko wadda babu Lionel Messi cikin kusan shekaru 20.

Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya tattauna da Jordi Alba na Barcelona a lokacin gasar cin kofin zakarun Turai a rukunin E tsakanin FC Barcelona da Benfica a filin wasan Camp Nou a birnin Barcelona da ke Spain ranar Talata 23 ga Nuwamba na shekarar 2021.
Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya tattauna da Jordi Alba na Barcelona a lokacin gasar cin kofin zakarun Turai a rukunin E tsakanin FC Barcelona da Benfica a filin wasan Camp Nou a birnin Barcelona da ke Spain ranar Talata 23 ga Nuwamba na shekarar 2021.

Kodayake Barcelona tana gaban kungiyar Benfica da maki biyu a rukunin E, amma samun nasara a Jamus ne kawai zai bai wa tawagar ta Xavi Hernandez garantin shiga zagayen wasan kwab-daya. Benfica za ta amshi bakuncin kungiyar Dynamo Kyiv, wadda tuni aka rabke ta a gasar.

GROUP F
Yayinda aka tabbatar da cewa kungiyar Manchester United ta zama zakara a rukuninta, yanzu an mayar da hankali akan ko wacce ce a tsakanin kungiyar Villarreal da Atlanta za ta rufa wa United kulub na Ingila baya a kungiyoyi 16 na zagaye na gaba. Za su fafata a Atlanta, inda wannan kulub na Italiya yake bayan kungiyar Villarreal wacce ta ke ta biyu a rukunin da ratar maki daya.

Nathaniel Clyne na Crystal Palace da Cristiano Ronaldo na Manchester United.
Nathaniel Clyne na Crystal Palace da Cristiano Ronaldo na Manchester United.

Don haka, Atlanta take bukatar samun nasara domin ta zama ta biyu a rukuninsu. Ita kuwa kungiyar Villarreal tana bukatar maki daya ne kawai ta tsallake gaci. Kungiyar Swiss ta Young Boys wadda Ralf Rangnick yake jagoranta, za ta yi tattaki zuwa gidan United, wanda shine wasan Ralf Rangnick na biyu tun lokacin da ya zama manajan riko, kuma yana bukatar yin nasara domin samun damar zama na uku a rukuninsu. Hakan zai kuma ba kungiyar sukunin shiga gasar League ta kulub din Europa. Amma kafin hakan ya tabbata, dole sai kungiyar Atlanta ta sha kashi a wasan da za ta yi.

GROUP G
A rukunin G kuma, ya zama dole kungiyar Wolfsburg ta yi galaba ko kuma a sallame ta. Za ta iya shiga cikin kulub 16 na karshe idan ta doke kungiyar Lille a gida wadda take sahun gaba a rukuninsu. Idan hakan ya tabbata wadda ta yi galaba a tsakanin kungiyar Salzburg da Sevilla a Austria za ta kasance zakara a wannan rukuni da kungiyoyin suke tafiya kafada-kafada. Lille tana da maki 8, Salzburg 7, Sevilla 6 yayin da ita kuma Wolfsburg take rufa masu bayan da maki 5.

Jerome Roussillon na Wolfsburg da Lucas Ocampos na Sevilla.
Jerome Roussillon na Wolfsburg da Lucas Ocampos na Sevilla.

Da kamar wuya, Kungiyar Wolfsburg ta Jamus ta zo matsayi na uku a rukunin. Ba’amurike kuma dan wasan gaba Timothy Weah ba zai samu fafata wasan da kungiyar Lille za ta yi ba a Wolfburg mai matukar mahimmanci saboda rauni da yake da shi a cinya. Amma zakarun Faransa watau Lille za su tsallaka zuwa zagayen wasan kwab-daya idan ba a doke su a wasan na gaba ba. Ita ma kungiyar za ta fafata a Jamus ba tare da ‘yan wasanta Jonathan Bamba da Xeka wadanda aka dakatar ba.

GROUP H
Har yanzu ba a tantance zakara a rukunin H ba, yayin da Chelsea da Juventus kowacce ke da maki 12, wanda hakan ya ba su tabbacin cewa sun tsallaka zuwa cikin kungiyoyi 16 na karshe. Chelsea mai kare kambun gasar, za ta iya kasancewa sahun gaba a rukunin idan ta yi galaba akan Zenit ta St Petersburg.

Thiago Silva na Chelsea ya mayar da martani yayin wasan kwallon kafa na gasar Premier ta Ingila tsakanin West Ham United da Chelsea a filin wasa na London da ke Landan, Asabar, 4 ga Disamba, 2021.
Thiago Silva na Chelsea ya mayar da martani yayin wasan kwallon kafa na gasar Premier ta Ingila tsakanin West Ham United da Chelsea a filin wasa na London da ke Landan, Asabar, 4 ga Disamba, 2021.

Juventus kuma za ta amshi bakuncin kungiyar Malmo, wadda take tashe, har ta rike kambunta a League din kasar Sweden a karshen mako. Har yanzu akwai sauran tsalle, duk da yake Zenit ta samu tabbacin zama ta uku a rukuninsu, wanda hakan zai ba ta sukunin shiga gasar kwab-daya ta Europa League, ita kuma kungiyar Malmo za ta kasance ta karshe.

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya mayar da martani a lokacin gasar wasan Premier League ta Ingila tsakanin kungiyar West Ham United da Chelsea a filin wasan London da ke birnin Londan ranar Asabar 4 ga watan Disamba a shekarar 2021.
Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya mayar da martani a lokacin gasar wasan Premier League ta Ingila tsakanin kungiyar West Ham United da Chelsea a filin wasan London da ke birnin Londan ranar Asabar 4 ga watan Disamba a shekarar 2021.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG