Accessibility links

Sanata Ahmad Lawal Daga Jahar Yobe Ya Koka

  • Halima Djimrao

Jaridun ranar 30 ga watan Satumba, 2013 da kanun labaran su akan harin da aka kaiwa Kwalejin Noma ta jihar Yobe,.

Sanata Ahmad Lawal ya ce matakin sojan da aka dauka a game da al'amarin Boko Haram ba ya magani.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin cewa akwai bukatar dawo da sadarwar wayar salula a jahar Borno don hakan zai taimaka wajen bayar da labarai cikin gaggawa da samun dauki, hakan nan kuma za a samu raguwar mutanen da ke zuwa wasu garuruwa domin yin waya wadanda a wasu lokuta kan shiga haduran da ke rutsawa da rayukan su. Shi ma dan majalisar dattaban Najeriya mai wakiltar jahar Yobe Ahmad Lawal ya tada wannan magana a gaban majalisar domin ya ja hankalin gwamnati tarayya kan bukatar yin garambawul game da yadda take tinkarar dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas. A tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu el-Hikaya, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana hujjojin shi kamar haka:

XS
SM
MD
LG