Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Naira Milyan 420 Da Nufin Taimakawa Wadanda Rikicin Zabe Ya Rutsa Da Su A Jihar Adamawa


Jami'an tsaro suke wuce gusa da wasu gine gine da aka kona sakamakon tashe tashen hankula a Najeriya.
Jami'an tsaro suke wuce gusa da wasu gine gine da aka kona sakamakon tashe tashen hankula a Najeriya.

Kwamitin raba taimakon kudi Naira Milyan 420 da gwamnatin tarayya ta bayar ya fara aikinsa a jihar Adamawa.

Gwamnatin tarayya ta bada Naira milyan 420 domin taimakawa mutane kamar metan a jihar wadanda tarzomar da ta taso bayan zaben shugaban kasa da aka yi a 2011 ta rursa da su.

Wannan shine karo na farko tun bayan rikicin shekaru biyu kenan d a wadanda suka yi hasarar rayuka da duniya suke ganin gudumawa ta farko. Adamawa tana cikin jihohi kamar hudu a arewacin Najeriya da rikicin ya shafa. Sauran jihohin sune Buachi, Kaduna da kuma Sokoto.

Borin ya biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, wanda ya nuna cewa shugaba Goodluck Jonathan ya sami gagarumar nasara. Abinda ya janyo zargin cewa an tafka magudi dalilinda masu zanga zangar suke ganin shugaban kasa ya sami nasara.

Da yake magana da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, a Yola, shugaban kwamitin raba kudaden Alhaji Mohammadu Ajuju Jimeta, yace wannan ba diyya ba ce, domin idan mutum yayi bari, ba zai iya ya kwashe duka ba, saboda haka wannan ba diyya bace, tallafi ne ga wadanda suka yi hasara lokacin da aka yi rikicin.

Wadanda suka amfana karkashin shirin a karamar hukumar Yola ta arewa kamar su Halliru Umar, da Samuel Onora sun bayyan farin cikinsu da samun wannan tallafi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG