Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shawo Kan Bazuwar Makamai a Najeriya


Makaman Da Yan Sanda Suka Kwace Daga Wasu Bata-Garin da ke samar wa ‘yan bindiga da sauran bata-gari a jihohin Taraba da Benue manyan bindigogi da harsasai da ake amfani da su wajen kai wa jama’ar da ba su ji -ba su gani hari a kauyukan jihohin.
Makaman Da Yan Sanda Suka Kwace Daga Wasu Bata-Garin da ke samar wa ‘yan bindiga da sauran bata-gari a jihohin Taraba da Benue manyan bindigogi da harsasai da ake amfani da su wajen kai wa jama’ar da ba su ji -ba su gani hari a kauyukan jihohin.

Biyo bayan yawaitar makamai a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba, Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci shugabannin rundunonin tsaron kasar su bayyana gabanta.

A kokarin Majalisar Dattawa na samar da hanyar da za a bi wajen gano tare da daukar matakin hana yaduwar makamai a fadin kasar, shugaban Majalisar Abubakar Bukola Saraki, ya ce dole ne a shawo kan yadukar makaman a akasar.

Sai dai kuma kakakin rundunar sojojin Najeriya, Janar John Agim, na ganin wannan bincike ne da yakamata ‘yan sandan kasar su gudanar, don gano ta wacce hanya makaman ke shiga Najeriya.

Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano, Kanar Aminu Isah Kwantagora, ya ce tun lokaci da rundunar hadakar ta soviet union ta rushe, kowanne soja ya koma kasarsa suka bar makamansu, hakan yasa masu fataucin makamai suka bazu suna cin karensu babu babbaka.

Haka kuma lokacin da aka kashe shugaban kasar Libiya Mohammad Gaddafi, makamai sun kwarara kasashen yammacin Afirka.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG