Accessibility links

Shekarau Yayi Mana Azarbabi - inji 'Yan Siyasar Borno

  • Garba Suleiman

Malam Ibrahim Shekarau (File Photo)

'Yan siyasa a Borno sun bayyana kalamun Shekarau na cewa watakila ba za a iya gudanar da zabe a jihohin dake fama da tashin hankalin Boko Haram ba a zaman shisshigi da rashin tunani

Shugaban jam'iyyar PDP na farko a Jihar Borno, Alhaji Ahmed Ashemi, ya bayyana kalamun da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, yayi cewar watakila ba za a iya gudanar da zabe a jihohin da ake fama da rikici, cikinsu har da Jihar Borno, ba, da cewa azarbabi ne, kuma wanda aka yi ba tare da tunani ba.

A cikin makon nan, Shekarau ya furta cewa watakila zaben 2015 ba zai iya yiwuwa a jihohin da suke fama da tashe-tashen hankulan 'yan Boko Haram ba.

Wannan kalami nasa yayi zafi ma 'yan Jihar Borno wadanda suka ce akwai sauran akalla watanni 10 kafin zaben, kuma idan har tsohon gwamnan na Kano yana tunanin cewa za a ci gaba da fama da wannan matsalar rashin tsaro har zuwa lokacin ne, to bai yi musu adalci ba.

"Ban ji dadin wannan furucin ba, domin ana kokarin murkushe wadannan 'yan tawaye. Saboda haka idan...zaben da (ba) za a yi ba sai nan da wata 9 ko 10 za a yi, amma yana hasashe a yau cewa ba za a yi zaben ba, yana hasashe cewa ba za a yi zabe ba, watau an sallamar wa Boko Haram ko 'yan ta'adda wadannan jihohin," in ji Alhaji Ahmed Ashemi.

Yace ba zai yarda kowane mahaluki ya sanya siyasa cikin halin da al'ummar Borno suke ciki ba, duk da cewa jam'iyyarsu daya ce.

Da aka tambaye shi ko yaya zasu yi idan har gwamnatin tarayya ta ce ba za a yi zaben na 2015 a Borno ba, sai Alhaji Ashemi ya kada baki yace, "sai mu ce Allah Ya isa."

Alhaji Mohammed Bukar, daya daga cikin 'yan siyasar Borno, yace ai kwanakin nan aka gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Yobe, kuma ana iya gudanar da irin wannan zabe nan da makonni biyu a cikin Jihar Borno.
XS
SM
MD
LG