Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Mayar Da 'Yan Gudun Hijirar Burundi Gida Ya Salwantar Da Rayuka


Wasu 'yan kasar Burundi da ake shirin mayar da su kasarsu daga Jamhuriyar Dimokradiyar Conko, ranar 31 ga watan Janairu 2017. (VOA/Christophe Nkurunziza)

Wani shirin mayar da 'yan gudun hijirar kasar Burundu zuwa kasashensu na asali daga kasar Congo ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 30.

Dakarun kasar Congo sun kashe akalla ‘yan gudun hijirar Burundi 36, kana sun jikkata sama da 100.

Wannan arangama ta faro ne a karshen makon nan, sanadiyar wani shiri na mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa kasashensu na asali, kamar yada jami’ai da masu fafutuka a cikin gida suka tabbatar.

Sojoji da ‘yan sanda sun bude wuta akan ‘yan gudun hijirar a lokacin da su, ‘yan gudun hijirar suka yi yunkurin kubutar da wasu ‘yan uwansu da aka kama a wani gari da ake kira Kamanyola, da ke gabashin kasar ta Congo wacce ke da iyaka da Burundi.

Rahotanni sun ce, dakarun sun yi yunkurin tarwatsa ‘yan gudun hijirar ta hanyar yin harbi a sama, amma haka ba ta cimma ruwa ba, inda har ta kai ga ‘yan gudun hijirar suka fara jifan dakarun da duwatsu, kamar yadda ministan cikin gida kasar ya fada.

Alfred Rukungo, wanda ya shaida hargitsin ya ce, duk da cewa sojojin sun jikkata da dama daga cikin ‘yan gudun hijirar, ba su daina bude wutar ba.

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira a Majalisar Dinkin Duniya, ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana kaduwa da bakin cikinta kan wannan al’amari.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG