Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Ce Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC Ya Farfado Da Kimarta


Shugaban rikon kwarya na APC Mai Mala Buni, hagu tare da shugaba Buhari, dama (Instagram/Mai Mala

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kwamitin rikon jam’iyyarsa ta APC karkashin shugabancin gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya farfado da kimar jam’iyyar musamman ta bangaren shiga tsakani da sasanta ‘ya’yan jam’iyyar da suke rikici da juna a matakin jihohi.

Shugaban ya ce aikin kwamitin rikon ya kara wa jam’iyyar APC mai mulki daraja da karfi sabanin yadda jam’iyyar take a baya.

Bayan shafe tsawon lokaci ana kai komo dangane da batun gudanar da babban taron jam’iyyar da zai samar da shuwagabannin jam’iyyar daga matakin tarayya zuwa kasa, daga karshe dai jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta na kasa a ranar Asabar 26 ga watan Maris da mu ke bankwana da shi.

Babban taron wanda ya gudana a dandalin Eagle Square da ke birnin tarayyar kasar Abuja, ya sami halartar jiga-jigan jam’iyyar ciki har da shugaban kasar Muhammadu Buhari, mataimakinsa, farfesa Yemi Osinbajo, shugabannin majalisun dokokin kasar, Sanata Ahmed Lawan, Femi Gbajabiamila da dukkan gwamnoninta sai kuma akasarin ‘ya’yan jam’iyyar ’yan majalisu da ma mambobinta da suka zo daga duk fadin kasar.

A lokacin jawabinsa, shugaba Muhammadu Buhari ya tabo batutuwa da suka hada da yadda kwamitin riko na jam’iyyar ya farfado da kimarta, nasarar samun gwamnoni uku gada wata jam’iyyar suka sauya sheka zuwa cikin APC, samun sabbin mambobi a jam’iyyar APC da su ka yi rajista lamarin da ya kai adadin mambobinta a halin da ake ciki suka dara miliyan 40 da dai sauran nasarori.

Shugaba Buhari ya kuma jaddada mahimmancin hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar don tunkarar babban zaben shekarar 2023 mai gabatowa inda ya bukaci a guje wa fadawa cikin sabbin rikice-rikicen cikin gida don gudun abun da ka biyo baya da za su iya kawo cikas a samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Kazalika, duk da cewa wasu yan siyasa na ganin shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban jam’iyyarsa ta apC, shugaban a yayin jawabinsa ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar da su guji kakaba ’yan takara da zasu saya mu su a zabe mai zuwa.

A wani bangare kuma, wasu gwamnonin jam’iyyar APC na ci gaba da taya sabon shugabansu murnar samun kujera mafi mahimmanci a jam’iyyar, su na masa fatan alkhairi.

Idan ana iya tunawa tun karshen shekarar 2021 ne ake ta rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Nasarawa , Abdullahi Adamu ne dan takarar kujerar shugaban APC da shugaba Buhari ya amince da shi.

A cikin jerin mutane da suka bayyana aniyarsu ta neman kujerar shugabancin jam’iyyar APC, mutane 7 suka sayi tikiti wadanda suka hada da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura, tsohon gwamnan jihar Buniwai, Sanata George Akume, tsohon gwaman jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, Sanata Sani Musa Muhammad, Etsu Muhammad, Turaki Sani Muhammad da Sanata Abdullahi Adamu da ya dare kan kujerar.

XS
SM
MD
LG