Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Cika Shekara 79


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

Bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban na Najeriya ya riske shi yayin da yake ziyarar aiki a birnin Santambul na kasar Turkiyya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekara 79 da haihuwa a ranar Juma’a.

Kakakin shugaban Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wani rubutu da ya wallafa wanda ya tabo nasarori da kalubalen da gwamnatin ta Buhari ta fuskanta.

Buhari kan yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a duk ranar 17 ga watan Disamba.

“Cikin shekaru 6 da ya kwashe a matsayinsa na shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu nasarori da dama. Amma an fuskanci wasu kalubale da za a magance su cikin watanni 18 da suka rage kafin ya bar ofis.”

Ziyarar Shugaba Buhari a Kasar Turkiyya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:38 0:00

Ziyarar Shugaba Buhari a Kasar Turkiyya

Zagayowar ranar haihuwar shugaban ta riske shi yayin da yake ziyarar aiki a birnin Santambul na kasar Turkiyya.

A ranar Alhamis Muhammadu Buhari ya bar birnin Abuja don halartar taron koli da zai tattauna kan huldar kasashen Afirka da kasar ta Turkiyya.

Wannan shi ne karo na uku da za a yi makamancin wannan taro tsakanin kasashen nahiyar ta Afirka da kasar ta Turkiyya.

XS
SM
MD
LG