Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Jami’an Ofishin Jakadancin Amurka  


Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya
Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana takaici game da kisan wasu jami’an ofishin jakadancin Amurka biyu da ‘yan sandan Najeriya biyu, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra. 

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin fadar shugaban Najeriya Garba Shehu, shugaba Buhari ya ce ya yi matukar bakin cikin jin labarin kisan ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka biyu da ‘yan sandan Najeriya biyu da ke musu rakiya.

"A mawuyacin yanayin da iyalan wadanda aka kashe suka samu kansu a ciki, da ofishin jakadancin Amurka da ma rundunar ‘yan sandan Najeriya, ina mika sakon ta’aziyyar al’umar Najeriya bisa ga wannan mummunan lamari da ya faru,” a cewar Buhari.

Hakazalika, an yi wa shugaba Buhari bayani game da kisan gillar da aka yi wa wasu mutane da yawa a garin Bwoi da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato, da kuma kisan da aka yi wa wasu mazauna kauyen Adaka a karamar hukumar Makurdi da garin Ijaha a karamar hukumar Apa duk a jihar Binuwai.

“Mun yi bakin cikin abinda ya faru da jami’an ofishin jakadancin Amurka, da rundunar ‘yan sandan Najeriya da al’ummomin wasu yankunan jihohin Filato da Binuwai, kuma mun kudiri aniyar gano wadanda suka kai hare-haren tare da hukuntasu. Allah ya yi ta’aziyya ya kuma ba iyalan mamatan ikon jure wannan rashi,” a cewar sanarwar.

XS
SM
MD
LG