Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Yayi Ganawar Sirri da IBB A Minna.


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Shugaban Kasar Najeriya Dr. Goodluck Jonathan, yayi wata ganawa ta sirri da tsohon shugaban kasa janaral Ibrahim Badamasi Babangida, a gidansa dake Minna, ganawar dai da bata wuce tsawon sa’a daya ba anyitane batare da manema labarai ba.

Kodayake dai babu wani bayani game da makasudun wannan ziyara da shugaba Jonathan ya kaiwa Babangidan, amma dai masu nazarin al’amurra na ganin tana da nasaba da ‘kalubalen tsaro daya addabi kasar da kuma watakila shugaba Jonathan yana kamun kafane game da babban zabe mai zuwa a kasar.

Tsohon gwamnan Kano da Benue alokacin Mulkin soja Kanal Aminu Isa Kwantagora, ya fadi tabakinsa game da wannan ziyara, inda yace, “to duk abinda muke bukatane don muna cikin siyasa, kuma muna cikin matsalar tsaro, to dole ne in a kace shuwagabanni kamar haka sun hadu to dole ne ansan abubuwan nan biyu za’a tattauna ne.” yakara da cewa wannan tattaunawa nada amfani kwarai da gaske dolene kasarmu ta cigaba a fanin siyasa da tsaro, idan kuma abin da suka tattauna akai kenan to Alhamdulillahi.

Shugaban kwamitin labarai a majalisa dokokin jihar Niger honorable Bello Agwara yayi tsokaci game da wannan ziyara. Inda yace, “wannan zaman yakamata ace tunda dadewa akayi wannan zaman koda kuwa ko wanne irin zamane, amma bai kamata ba ace sai lokacin da aka ga zabe ya karato wanda nan da wata daya za’ayi zaben, sannan ace gashi Jonathan zai zauna dashi ainishin Ibrahim Badamasi Babangida, duka da kamar yadda nace bamusan abinda zasu tattauna ba amma kasan mutane dayawa zasuyi sharhi kuma zasu ga kodan yana neman goyon bayane saboda neman samun nasarar zabe mai zuwa na shekara ta 2015, indan kuma bashi bane meyasa akayi zaman yanzu ba’ayiba tuntuni ba. Kowa yasan halin damuke ciki a wannan kasar, kuma ansan kashe-kashen da akeyi awannan kasar, kuma abin nan ya addabemu musamman ma ‘yan Arewacin Najeriya.”

Komade mekenan zayarar ta shugaba Jonathan ga Babangidan, tazone a dai dai alokacin da tura takai bango game da lamarin tsaro a kasar dakuma yadda aski yazo gaban goshi gameda babban zaben da ‘yan Najeriya zasu zabi sababbin shugabannin Kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG