Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Moon Jae-in Ya Bukaci Kim Jong Un Ya Tattauna Kai Tsaye Da Washington


Wadansu suna gudu a Singapore Inda Trump Zai gana da Kim
Wadansu suna gudu a Singapore Inda Trump Zai gana da Kim

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in yayi kira ga takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya tattauna kai tsaye da Washington domin ceto shirin ganawar da aka yi niyar yi kan batun makaman nukiliya,ranar goma sha biyu ga watan Yuni da Amurka.

Shugaban Moon ya yi wannan kiran ne yayin ganawar ba zata da shugabannin kasashen Koriyan biyu suka yi karo na biyu jiya asabar.

Koriya ta Arewa ce ta bukaci ganawar tsakanin Kim da Moon bayan soke ganawar da aka yi shirin gudanarwa a Singapore, da shugaban Amurka Donald Trump yayi ranar alhamis.

Moon yayi hira da manema labarai bayan ganawarsu da Kim a kauyen Panmunjom dake bangaren Arewa na kan iyakar koriyawan, inda shugannin suka gana a watan Aprilu.

Yace “Mun amince cewa ya kamata a yi ganawar ranar goma sha biyu ga watan Yuni cikin nasara, kuma bai kamata a dakatar da yunkurinmu na raba yankin Koriyan da makaman nukiliya ba. Mun amince mu ba juna hadin kai dangane da haka.”

Jiya asabar shugaba Trump ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne a gudanar da taron da aka soke.

Yace “Ina jin akwai kyakkyawar fata sosai, ina tsammani mutane suna so su gani ko zamu gana, ko zamu iya cimma burinmu. Idan muka iya ganawa muka kuma yi nasarar raba yankin Koriya da makaman nukiliya, zai zama Alheri ga Koriya ta Arewa, Alheri ga Koriya ta Kudu, Alheri ga Japan, Alheri ga duniya da kuma Amurka.”

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG