Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Fasa Ganawa Da Shugaban Koriya Ta Arewa


Shugaba Trump Da Shugaba Kim Jong Un

Shugaban Amurka, Donald Trump ya soke taron kolin da a da aka shirya za’ayi tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un a ran 12 ga watan Yunin wannan shekara.

A cikin wata wasikar da fadarsa ta White House ta sako a yau, Trump yace “a bisa la’akari da irin matsancin fushi da tsokana da ka nuna a cikin bayaninka na baya-bayan nan, ina ganin ganin bai dace ba muyi wannan taron da aka dade ana shiryawa.”

Soke taron na zuwa ne a daidai lokacinda Koriya ta Arewa din ke bada sanarwar rufe sansanin gwajin makamanta na nukiliya na Punggye-ri yau Alhamis domin nuna cewa da gaske take gamede kudurinta na dakatar shirin ta na kera makaman nukiliya kafin taron kolin da a da ake shirin yi tsakanin shugabannin KTA da Amurka.

Gwamnatin KTK ta yaba da matakin da KTA ta dauka da kanta, ba da tilasatawa ba, na dakatar da shirin makaman nukiliyar ta don taimakawa wajen ganin an kulla yarjejeniya da Amurka domin dakatar da shirin makaman nukiliyar ta kachokan, don ita kuma a cire mata takunkumi da Amurka ta sanya mata tare da kuma tabattar mata tsaron kasarta.

Sai dai kuma duk da yake rufe sansanin gwaje gwajen shirin Nukiliyar kachokan abin a yaba ne, masu fashin baki na kokwanton watakila ko hakan zai iya hana wa gwamnatin Kim Jong Un damar iya cigaba da gwaje gwajen makamanta na Nukiliya anan gaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG