Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Mubarak na Misra ya yi Murabus, Jama'a na ta Murna


Masu zanga-zangar kin gwamnati ke nan ke murna a Dandalin Tahrir saboda murabus din da Shugaba Hosni Mubarak ya yi.

Shugaba Hosni Mubarak na Misra ya yi murabus bayan zanga-zangar kwanaki 18 da Masarawa su ka yi, na neman kawo karshen shugabancinsa na tsawon shekaru 30.

Shugaba Hosni Mubarak na Misra ya yi murabus bayan zanga-zangar kwanaki 18 da Masarawa su ka yi, na neman kawo karshen shugabancinsa na tsawon shekaru 30.

Dubun dubatan Masarawa ne su ka bazu zuwa kan tituna cikin murna da farin ciki don yin bikin wannan sanarwar ta yau Jumma’a da Mataimakin Shugaban Kasa Omar Suleiman ya yi, wanda y ace an mika ikon na shugaban kasa ga hukumar soji. Gidan Talabijin na kasar y ace za a bayar da cikakken bayani an jima kadan a yau dinnan jumma’a kan yadda sojojin za su shugabanci kasar.

Dandalin Tahrir da ke birnin al-Khahira --- wanda nan ne ma bijirewar ta fi kamari --- ya barke da sowar shagulgula.

Dubban wadanda su ka yi zanga-zangar sun yi ta ihu cike da murna har bayan sa’a guda da jin sanarwar ta murabus din Mubarak. Mutane da dama sun yi ta daga tutucin Misra a sailinda wutar nuna alamar farin ciki k eta haskaka sararin subahana. Wasu dinbin mutanen kuma sun yi ta shagulgula a kan titunan birnin Askandariyya, inda motoci da dama su ka yi ta busa. A sauran biranen ma an yi ta shagulgula.

Wannan ‘yar takaitacciyar sanarwar ta Suleiman ta zo ne bayan sama da makonni biyu na zanga-zangar kin gwamnati. Mataimakin shugaban kasar ya ce Mr. Mubarak ya yi la’akari ne da ‘mawuyacin halin da kasar ta fada ciki.’

Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito jami’an gwamnati na cewa Mr. Mubarak ya bar babban birnin kasar zuwa gidansa da ke mashakatar Sham El-Sheikh da ke kusa da gabar Bahar Maliya.

A halin da ake ciki kuma, dab da kammala rubuta wannan labarin, Shugaban Amurka Barack Obama, ya kammala jawabinsa kan murabus din da Mubarak ya yi, inda ya yi na'am da al'amarin ya kuma ce Amurka za ta cigaba da hada hannu da gwamnatin Misra.

Kafin nan dai Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce murabus din shugaban Misra Hosni Mubarak ya bude wani sabon babi a tarihi.

Ya yi wannan maganar ce a jihar Kentucky ta Amurka, gabanin jawabin Shugaba Barak Obama a birnin Washington.

Biden y ace tun farkon wannan zanga-zangar Amurka ta dage kan cewa Masarawa ne za su zabi makomar Kasarsu.

Y ace Amurka ta tsaya kan muhimman manufofinta lokacin da ake zanga-zangar --- ciki har nuna cewa duk wani yinkurin musguna wa masu zanga-zangar baa bin amincewa ba ne, da kuma kiraye-kirayen a mutunta ‘yancin Masarawa tare da biya masu bukata. Y ace Amurka ta kuma bukaci shirin gyare-gyare a siyasar Misra ya zama mai dorewa a kuma fara tattauna hanyar komawa ga tafarkin dimokaradiyya.

‘Yan Majalisan Tarayyar Amurka sun yaba da murabus din da Mubarak ya yi. Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa Harry Reid y ace ya yi farin ciki da yadda Mubarak ya ‘saurari mutanen Misra.’ Dan Majalisar Dattawa dan Republican John McCain ya yaba da matakin da Mubarak ya dauka. McCain, wanda shi ne dan takarar shugaban kasar jam’iyyarsa a zaben 2008, y ace tarihi zai nuna cewa matakin da shugaban na Misra ya dauka na baya bayannan shi ya fiye wa kasarsa.

Amurka na bai wa Misra taimako ta fuskar soji da ya kai sama da dala miliyan dubu dari da uku a kowace shekara. Wasu ‘yan Majalisar Dokokin Amurka sun bukaci a daina bayar da wannan taimakon muddin aka yi jinkirin gyare-gyare a gwamnatance a kasar.

XS
SM
MD
LG