Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ba Zai Halarci Wasu Tarukan G-7 Ba


Shugaba Donald Trump

Yayin da ake shirin gudanar da taron kolin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya G-7 a kasar Canada, shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki mai masaukin baki, frayim-ministar kasar ta Canada, Justin Trudeau, kana fadar White House ta ce Donald Trump ba zai halarci wasu tarukan ba.

A wani sakon Twitter da ya fitar da yammacin jiya Alhamis, Trump ya zargi firayim ministan Canada da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da karawa Amurka haraji mai dimbin yawa da kuma saka shingen tattalin arziki da Amurka.

Trump ya kuma ce Trudeau yana bayyana fushinsa game da huldar cinikayar kasashen ketare.

A cikin daren jiya Alhamis, Trump ya sake kafe wani sakon Twitter, inda ya gargadi Kungiyar Tarayyar Turai da Canada da su fidda haraji da shingaye da suka saka ko kuma Amurka tasa kafar wando daya da su.

Sakon Trump ya biyo bayan barazana da Macron ya yi ne cewa za a fidda Amurka daga kudurin da kasashen G-7 zasu fitar a karshen taron kolin da ake yi a birnin Charlevoix mai tsaunuka.

A cikin sakon Twitter da shima ya aike da Faransaci da kuma Turanci, Macron ya ce yayin da Trump bai damu da ya kebe kansa, toh su kuma sauran shugabanni shidan ba zasu damu su sanya hannu a kan kudurin bayan toron su kadai ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG