Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka na Nazarin Saka Koriya ta Arewa a Jerin Kasashen Dake Goyon Bayan Ta'addanci


Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

Shugaban Amurka Barack Obama yace gwamnatinsa tana sake nazarin ko ta sake saka koriya ta Arewa a jerin kasashe dake goyon bayan ta'addanci, bayan harin da kasar ta kai kan na'urorin komfuta kamfanin hada fina-finai na sony, al'amarin da jamia'an Amurka suke aza lafin kan kasar mai bin tafarkin kominisanci.

Da yake magana cikin shirin talabijin na CNN mai suna "State of Nation", Mr. Obama yace bai dauki satar shigar na'urorin komfutocin kamfanin Sony A matsayin ayyana yaki akan Amurka ba, amma alamace ta irin hasarar kudi masu yawa da irin barnar da za'a iya aikatawa ta wannan fanni.

Koriya ta arewa ta musanta cewa itace ta kaiwa kamfanin Sony hari kan na'urorinta, wanda daga bisani ta fallasa wasikun email da wasu bayanan-sirri na kamfanin a dandalin internet.

Wanda suka saci shiga na'urorin komfutocin na Sony, sun kira kansu "Baraden zaman lafiya", daga nan suka yi gargadin cewa "mummunar makoma" tana dakon duk wanda yaje kallon siliman mai suna "The Interview" da turanci, a cikin siliman, hukumar leken asiri ta Amurka CIA, tayi hayan 'yan jarida biyu su kashe shugaban kasar Koriya ta arewa, kim Jong Un.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG