Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Zai Gana da Shugaban Mexico


Sabon shugaban Amurka Donald Trump
Sabon shugaban Amurka Donald Trump

Fadar White House ta shugaban Amurka tace shugaba Donald Trurmp zai gana ranar 31 ga watan nan na Janairu da shugaban Mexico Enrique Pena domin su gudanar da shawarwari kan bakin haure, da kuma sake duba jarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen biyu da ake kira NAFTA.

Shugaba Trump yace,shugaban na Mexico gagarumin mutum ne,kuma ina jin zamu sami kyakkyawar sakamako tsakanin Mexico da Amurka da kuma duk wadanda lamarin yashafa," inji Trump.

Haka nan sabon shugaban na Amurka yace yana shirin zai gana da shugaban Canada Justin Trudeau.

Shugaban na Amurka yayi yakin neman zabensa tareda alkawarin zai sake gudanar da shawarwari da aka kulla ta yarjejeniyar cinikayar da ake kira NAFTA.

Haka nan Mr. Trump yayi ba'a ko shagube kan mutane fiyeda milyan daya da suka fito ranar Asabar domin gudanar da zanga zangar nuna adawa da gwamnatinsa. Yace, "na kalli zanga zangar ranar Asabar, amma na aza bamu juma da yin zabe ba!" Inji Trump ta shafinsa na Twitter daga Fadar White House, gidansa na shekaru hudu masu zuwa. Me yasa mutanen nan basu yi zabe ba? Sanannun mutanen nan ne suka dama harkoki sosai."

XS
SM
MD
LG