Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Iran Ya Musanta Zargin Da Amurka Ke Yiwa Kasar Sa


Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad ya na gaisawa da manema labarai a birnin Tehran.

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad ya ce Iraniyawa wayayyun mutane ne

Shugaban kasar Iran ya musanta zargin Amurka na cewa da hannun gwamnatin kasar Iran din a cikin wata makarkashiyar neman kashe jakadan kasar Saudiyya a nan Amurka.

A yau Lahadi shugaba Mahmoud Ahmadinejad ya fada cewa Iraniyawa mutane ne masu wayewar kai, kuma ba sa bukatar yin amfani da hanyar yin kisan gilla.

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad
Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad

Babban shugaban addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya fada a jiya Asabar cewa ikirarin na Amurka ba shi da kan gado, sannan ya zargi Amurka da yin zargin da ba tushe akan wasu ‘yan kasar Iran kalilan da ke kasar Amurka a kokarin ta na neman maida Iran saniyar ware.

XS
SM
MD
LG