Accessibility links

Yan sanda sun kama mutane da dama cikin masu zanga zanga da dama a birnin New York


Yan sanda sun kama wadansu masu zanga zaga a birnin New York.

Yan sanda a birnin New York sun kama sama da mutane saba'in da suka hada da wadansu daga cikin masu zanga zanga da suka yi dafifi a fitaccen dandalin nan na birnin NY da ake kira Times Square, yayin zanga zangar da ta bazu a fadin kasashen duniya ta nuna adawa da babakere da kuma handamar manyan kamfanoni.

Yan sanda a birnin NY sun kama sama da mutane saba'in da suka hada da wadansu daga cikin masu zanga zanga da suka yi dafifi a fitaccen dandalin nan na birnin New York da ake kira Times Square, yayin zanga zangar da ta bazu a fadin kasashen duniya ta nuna adawa da babakere da kuma handamar manyan kamfanoni.

Yan sanda da suka yi shirin ko ta kwana wadansu a kan dawakai sun yi kokarin tura mutanen su fita daga dandalin da zumar tarwatsa taron.

Wannan na daya daga cikin zanga zanga da dama da aka gudanar a wurare da dama a Amurka da kuma sauran kasashen duniya jiya asabar, wanda ya sami asali daga yunkurin nan da aka ba lakabi “Occupy Wall Street”.

Fitaccen mai shirya fina finai a Amurka Micheal Moore ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ya shiga sahum masu zanga zangar a Wall Street domin nuna goyon bayanshi ga wannan yunkuri na nuna fushin talakawa kan manyan ‘yan kasuwa.

Yan sanda a birnin Rome sun yi amfani da barkonon tsohuwa da mesar ruwa, yayinda wasu tsirarru daga daruruwan masu zanga zanga kan tituna suka balle suka shiga fasa tagogi da kone kone. An kuma baza ‘yan sanda a babban birnin kasar Italiya.

A birnin London kuma, an yi arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga daga cikin daruruwan mutane da suka taru kusa da majami’ar St. Paul.

An kuma yi zanga zanga a kasashen Australia, da New Zealand. Da Spain da jamus da kuma Faransa inda membonbin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki G20 suke taro a birnin Paris, domin tattaunawa a kan matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a kasashen turai.

Masu zanga zanga da dama suna nuna adawa ne da gibin dake tsakanin masu arziki da talakawa, yayinda suke kiran kansu kashi casa'in da tara bisa dari akasin kashi daya bisa dari na wadanda suka ce, arzikin duniya ke hannunsu.

XS
SM
MD
LG