Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasa Ya Kori Magajin Gari Saboda Sakaci


Shugaba Isuhu Muhammadu na jamhuriyar Nijar ya nuna bacin rai da rashin tsaftar birnin Yamai.

A jamhuriyar Nijar gwamnati ta kori babban magajin garin yamai Hassan Saidu, daga aiki kwanaki kadan bayan da shugaban kasa Isuhu Mahamadou, ya gudanar da ziyara a birni Yamai, a karshe ya nuna bacin rai a game da halin kazantar da birnin Yamai ke ciki saboda sakacin.

Taron majalisar Ministoci kasar ta Nijar da aka gudanar jiya alhamis ne ya bada sanarwar dakatar da magajin garin na Yamai, Hassan Saidu, daga aiki wanda a baya bayan nan a fili karara Shugaba Isuhu ya nuna bacin rai kan yadda shi da mukarrabansa suka jifa birnin Yamai cikin kazanta.

Wani mazaunin birnin Yamai kuma Malam Nasiru Saidu, yay aba da wannan mataki na shugaban kasar Nijar, yana mai cewa abinda suke fata shine kada abin ya tsaya kan mutun daya ko biyu ba a ci gaba da bibiyar duk wani ma matsayi da bashi tafiyar da aikin sa yadda ya kamata.

Sai dai wani masanin doka Metri Lawan Abdulrahaman, na ganin cewa dakatar da magajin garin ya sabawa doka yana mai cewa doka tace kananan hukumomi shugaban karamar hukuma ne ke sa ido akansu na gudumomi gwamna ne ke sa ido akansu tare da ma’aikatar cikin gida.

Amma a cewarsa irin wannan da ya faru mataki ne wanda shugaba kasa shine ya ganin da idonsa wanda kuma idan za a cire shi sai a bi matakin da doka ta shinfida daga mataki zuwa mataki.

Gwamnatin a wannan taron ta sanar da Koran babban magatakardanta Gandu Zakara, mai ofishin a fadar Firayminista, domin maye gurbinsa da mataimakin shugaban kotun tsarin mulkin kasa Abdu dan Galadima.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG